[{{mminutes}}:{{sseconds}}] X
Пользователь приглашает вас присоединиться к открытой игре игре с друзьями .
Обычный хауса
(2)       Используют 8 человек

Комментарии

Ни одного комментария.
Написать тут
Описание:
Тексты на хаусе (Hausa), в среднем 210-270 символов, но некоторые подлиннее
Автор:
sashavirtual
Создан:
18 августа 2024 в 20:09 (текущая версия от 24 мая 2025 в 15:50)
Публичный:
Нет
Тип словаря:
Тексты
Цельные тексты, разделяемые пустой строкой (единственный текст на словарь также допускается).
Содержание:
1 Ganin kuma cewa an bayyana cewa: muhimmin gurin da ’yan-adam suka sa gaba shi ne, bayan sun kuɓuta daga tsananin iko da wahala, kowa ya sami damar faɗin ra'ayinsa kuma ya sa rai ga abin da zuciyarsa ta saka masa.
2 13. Kowane mutum na da hakkin yin kai-da-kawowa cikin ’yanci, ya ma zauna wurin da yake so a cikin wata ƙasa. Kowane mutum na da hakkin ya fita daga kowace ƙasa, har da ƙasarsu kuma yana da hakkin komowa ƙasarsu.
3 Sannan ya ce magana ce ta biyan bukata, kowa da manufarsa a siyasa kuma kowa na duba gajiyar da zai samu. "Idan mutum ya samu kofa babu wani laifi da korafe-korafe. Komai ka ga mu na yi mu na yi ne domin al'umma.
4 A cikin na'urorin sarrafa nesa na rediyo mara waya kamar drones, masu buɗe kofa na gareji, da tsarin shigarwa marasa maɓalli, siginar rediyo da ake watsawa daga na'urar sarrafawa suna sarrafa ayyukan na'urar nesa.
5 Ganin cewa ’yanci da adalci da zaman lafiya ba za su girku a duniya ba, sai in an amince da cewa: dukkan ’yan-adam suna da mutunci, kuma suna da hakkoki na kowa daidai da na kowa, waɗanda ba za a iya ƙwace musu ba.
6 Suna yin haka ne a bisa alƙawurra daban-daban da aka yi masu. Sai dai mafi yawan masu sauya sheƙar dai suna kafa hujja ne da rikicin cikin gidan jam'iyyun su, wanda suka ce ya tilasta masu ficewa domin samun mafita.
7 Gilashin gilashi da rufin aluminum da aka yi amfani da su don gine-gine a Cibiyar Ciniki ta Duniya suna da tsayayya da zafi, suna da tsayin daka kuma ba sa ƙonewa. Gine-gine suna amfani da tsarin sanyaya iska na VRV.
8 28. Kowa na da hakkin ganin an sami kyakkyawan shiri a cikin zaman jama'a da tsakanin ƙasashen duniya domin hakkokin nan da dukkan abubuwan da ’yanci ya ƙunsa waɗanda aka bayyana a cikin wannan jawabi su tabbata sosai.
9 "Sau dayawa wasu yara suna da burin su yi karatu har zuwa babban mataki amma kuma samun ƙarancin maki a JAMB na iya sauya karatunsu gaba ɗaya inda za a ga da sun gama makarantar sakadire, sai su koma suna wasu ayyuka".
10 Saboda haka yana da hakkin ya sami ’yancin kauda duk wani tsoro game da ra'ayoyinsa, da ’yancin neman labaru da sababbin ra'ayoyi, ya same su kuma ya baza su duk inda yake so ba tare da sanin iyaka ba, kuma ta kowace hanya.
11 16. Idan mace da namiji sun isa aure, suna da hakkin su auri juna su yi iyali, kuma za a yi auren ba tare da an rage wa waninsu darajarsa ta ɗan-adam ba saboda launin fatarsa ko don yana ɗan wata ƙasa ko kuma don addininsa.
12 Saboda haka ya ce dole a dinga samun addadin yara masu tarin yawa da suke samun ƙarancin maki a JAMB. "Za a ga yaro ya ci jarabawar shi na Waec amma kuma ya kasa cin jarabawar shi na JAMB ko ya sami ƙaramin maki." in ji shi.
13 Dalilin haka ne ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ɓangaren ilimi da JAMB su zauna kuma su sake nazari kan manhajar karatu ya kasance abin da ake karantarwa a makarantun sakandire shine ake tambaya a jarabawar JAMB ba ki ɗaya.
14 Cibiyar kuma tana da tsaron CCTV na ci gaba kuma tana amfani da damar sarrafa katin a duk yankuna. Akwai matakai uku na filin ajiye motoci a cikin hadaddun. Tsarin bangon labule da ginin ya yi amfani da shi ne Eurotech Facades.
15 A 110 metres (361 ft), Hasumiyar WTC mai hawa 24 1, wacce ta kai a shekarar 2015 ita ce taƙaitacciyar gini mafi tsayi a Najeriya, yayin da Hasumiyar BTC 2 ita ce gini mafi tsayin daka a Abuja, tana tsaye a 120 metres (394 ft).
16 1. Su dai ’yan-adam, ana haifuwarsu ne duka ’yantattu, kuma kowannensu na da mutunci da hakkoki daidai da na kowa. Suna da hankali da tunani, saboda haka duk abin da za su aikata wa juna, ya kamata su yi shi a cikin ’yan-uwanci.
17 "Idan muka duba za mu ga cewa rashin waɗannan kwamfutoci da yara ke amfani da su, ba a yawan koyar da su a makarantu saboda babu, kuma yanzu JAMB sai da ilimin kwamfuta saboda da ita ake rubuta jarabawar. Daktan ya ƙara da cewa.
18 Abubuwan da wannan jawabi ya ƙunsa su zamanto gurin da dukkan al'ummu da ƙasashen duniya suka haɗu a kansa kuma suka yi ƙoƙarin cimma, domin kowane mutum da kowane sashen jama'a wanda yake da wannan jawabi a ka ko da wane lokaci.
19 "Sai kawai na ci gaba da karatun nazarin addinin Musulunci, sau uku ina sake rubuta jarabawar JAMB, ina saka kwas ɗin da nake so, amma makina ba ya kaiwa, hakan nan na haƙura na gama karatun "Islamic studies" ɗin da suka ba ni.".
20 A Najeriya, jarrabawar JAMB ta kasance matakin farko da ɗalibai ke bi domin samun gurbin karatu a jami'o'i da sauran manyan makarantu. Duk da haka, sau da dama daliban da ke da burin zama likitoci, lauyoyi, injiniyoyi da sauransu.
21 Ganin cewa a cikin usular (takardar sharuɗa) al'ummu, ƙasashen duniya sun sake nuna amincewarsu da muhimman hakkokin ’yan-adam, da mutuncinsu, da darajar da waɗannan halittu suke da ita kuma a kan daidai-wa-daida ga namiji da mace.
22 12. Ba wanda wani zai shiga sha'aninsa na rayuwa, ko na iyali, ko na mahalli, ko na wasiƙu ba tare da yardarsa ba, ko kuma a ci masa mutunci ko ɓata masa suna. Kowa na da hakkin doka ta yi masa kariya game da irin waɗannan abubuwa.
23 Daktan ya ce JAMB tana da naƙasu sosai saboda manhajar karatun da yara suke rubuta jarabawar JAMB da shi ba shi bane manhajar karatun da ake karantar da su tun daga matakin sakandire ba. Manhajar karatun ya sha bamban sosai in ji shi.
24 Da yake jawabi, mai magana da yawun ƙungiyar, Ambasada Jamal Rushdi ya ce a hukumance an amince da gwamnatin da ke da jagorantar ƙasar a halin da ake ciki, yayin da aka jadadda cewa babu wata kofa ta amincewa da wata gwamnati ta daban.
25 Ya ce, ƙungiyar ta ƙasashen Larabawa zanta yi duk mai yiwuwa wajen dawo da zaman lafiya da kuma kare halastaciyyar gwamnati a Sudan, yayin da ta kira ɓangarorin da ke rikici da juna da su magance matsalolinsu ta hanyar amfani da siyasa.
26 "Da na ga sakamakon makin da na samu, a lokacin na san ba lalle burina ya cika ba." A ƙarshe, Maryam ta ce ta sauya kwas ɗin da take so daga fannin Likitanci zuwa fannin Biochemistry a wata jami'ar jiha saboda ƙarancin makin da ta samu.
27 Yadda al'umma ke so ne mahakunta za su tafiyar da mulkin kasa; za a san buƙatar al'umma game da mulki ta hanyar gudanar da zabe kan gaskiya lokaci zuwa lokaci, inda dukkan ’yan-ƙasa a zaman daidai-wa-daida muddin dai suna cikin sharaɗi.
28 Suka kuma ɗauki alkawalin yin ƙoƙari domin su kyautata wa ’yan-adam jin daɗin rayuwa a cikin suna ƙara walawa da ’yancinsu, ganin cewa ƙasashen da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙunsa sun ɗauki alkawalin cewa: tare da haɗin gwiwar Majalisar.
29 Ko shi da kansa ko ta hanyar aika wakilansa waɗanda ya zaba cikin ’yanci. Kowane mutum na da hakki a cikin sharaɗin daidai-wa-daida ya sami halin a ɗaukaka shi ya kama ragamar tafiyar da waɗansu ayyukan ƙasarsu na kula da harkokin jama'a.
30 Wani abun da ke bada mamaki dai shi ne yada lamura suka dau zafi tun kafin a kai ga lokacin neman zaben 2027. Menene gaskiyar zargin? Ana dai ganin watakil sauya sheka da jam'iyyar adawa ke yi zuwa APC na da alaka da lasa musu zuma a baka.
31 "Mu bama munafunci, gaskiya guda ce, mun fi wadanda ke boye-boye suna zagaye da cin amana". Dan majalisar ya kuma nuna babu batun cin amanar jam'iyyar da ta bashi kujerar Sanata, yana mai jadadda cewa komai ya yi saboda al'ummarsa ya ke yi.
32 Bukatun al'umma. Sai dai yayin da jam'iyyar APCn ke musanta zargin cewa ba ta yi wa sabbin amaren nata alƙawari kafin sauya sheƙar tasu ba, Sanata Suleiman Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu, ɗaya daga cikin waɗanda suka cire rigar adawa.
33 Wannan adadi kawo yanzu ya ninka wanda aka gani cikin shekaru 3 da suka gabata, abinda wataƙila baya rasa nasaba da halin da ƴan ƙasar ke ciki na matsin tattalin arziki, ta’addanci da kuma yadda ƴan siyasa ke shaƙe wuyan ƴan adawa a siyasance.
34 Ya maida himma ta hanyar tsarin makarantu da tarbiyya domin a ƙarfafa kiyayewa da waɗannan hakkoki da dukkan abubuwan da ’yancin ɗan-adam ya ƙunsa. Bayan haka a yi ƙoƙari ta hanyar ɗaukar matakai waɗanda za a rika ingantawa lokaci zuwa lokaci.
35 Duk wanda ƙwazonsa ya ba hali ya kamata a ba shi damar zuwa neman ilimin ƙoli ba tare da bambanci ba. Abin nufi ga ilimi shi ne: ya sama wa ɗan-adam jin daɗin rayuwa da ƙarfafa kiyayewa da hakkokinsa da muhimman abubuwan da ’yancinsa ya ƙunsa.
36 "Akwai yara da ni na gani, sun gama karatun sakandire suna neman shiga jami'a, sun yi JAMB sun saka kwasa-kwasan da suke so, amma ba su ci ba, yanzu haka sun zama waɗanda ba su gama karatu ba - sun ƙi su ci gaba da karatun." in ji Dr Abubakar.
37 8. Kowane mutum, idan ya ga za’a aikata abin da zai hana shi cin moriyar hakkokinsa waɗanda tsarin mulki ko dokar ƙasa ta tanada masa, yana da hakkin ya kai ƙara a gaban hukumar ƙasarsu wadda ke da mukamin yanke hukunci game da irin wannan laifi.
38 Dukkan ’yan-adam, ba tare da wani bambanci ba, suna da hakkin su sami kimar albashi da’ya idan aiki ɗaya suke yi. Duk wanda ke aiki na da hakkin ya sami albashi gwargwadon guminsa, wanda zai biya masa buƙatunsa na yau da kullum da shi da iyalinsa.
39 Kowace shekara, dubban matasa a Najeriya suna fuskantar irin wannan ƙalubale. Samun ƙarancin maki na jarabawar JAMB na saka mutane da dama su rungumi fannonin da ba su da buri a kansu wanda hakan ke sauya musu rayuwa da aiki, ba bisa muradinsu ba.
40 Wannan buri nata tun tana ƴar ƙarama take da shi, wanda ta samo daga girmamawa da take yi wa yayarta da ke aiki a wani asibiti a ƙauye kusa da Minna, Jihar Neja. Amma sakamakon maki 189 da ta samu a jarabawar bai kai makin shiga karatun likitanci.
41 Malam Bala ya ce zance na gaskiya ana yiwa 'yansiyasar mumunan zato, wanda idan aka bincika kowa na da dama da manufar da ya fi fifitawa. "Babu wani alkawari da aka yi musu, kowa matsayarsu daya a APC. Kawai zarge-zarge 'yan adawa marasa tushe ne".
42 Matsayin ɗan gudun-hijiran da doka ta hana a taɓa. Mutumin ba zai iya yin amfani da wannan hakki ba idan ana nemansa bayan an tabbata ya aikata babban laifi irin wanda doka ta hana ko wanda ya saɓa wa manufar Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙa'idodinta.
43 24. A game da aiki, kowane mutum na da hakkin ya sami hutu don ya shaƙata da musamman ƙayyadadden wa'adin aiki yadda ba zai raunana masa ba, kuma yana da hakkin ya sami dogon hutu lokaci zuwa lokaci wanda a cikinsa zai kasance yana karɓar albashinsa.
44 Misali mutum ya zauna cikin hausawa, da yarbawa, da inyamurai, kuma alhali a cikinsu akwai mugaye da nagari da macuta da 'yan iska da masu hali mai kyau, yana a matsayin ɗan kasuwa, batare da ɗaya daga cikinsu ya iya cutar da shi ba ko shi ya cuce su.
45 7. Kowa daidai yake da kowa a gaban doka, kuma kowa na da hakkin doka ta yi masa kariya ba tare da nuna bambanci ba. Kowane ɗan-adam kamar kowa, na da hakkin a yi masa kariya game da duk wani bambancin da zai saba wa matakan da ke cikin wannan jawabi.
46 Duk da cewa sauya sheƙa a fagen siyasar Najeriya ba baƙon al'amari bane, da alama wannan karon abin zai ci gaba da jan hankali musamman ta la'akari da yadda siyasar ke ƙara ɗaukar zafi tun ana saura aƙalla shekara biyu wa'adin gwamnati mai ci ya ƙare.
47 An watsa watsa shirye-shiryen rediyon kasuwanci na farko a ranar 2 ga Nuwamba, 1920 lokacin da Westinghouse Electric da Kamfanin Manufacturing Company ke watsa shirye-shiryen zaben shugaban kasa na Harding-Cox a Pittsburgh, karkashin alamar kira KDKA.
48 22. Kowane mutum, a matsayinsa na kasancewa ɗaya daga cikin halittun da jama'a ta ƙunsa, yana da hakkin a tabbatar masa da jin daɗin rayuwa ma'anar tabbatar wa ɗan-adam da jin ɗadin rayuwa shi ne: dangance da tsarin kowace ƙasa da halin da take da shi.
49 Kuma irin waɗanda suka kamaci ɗan-adam a cikin mutuncinsa. Bayan haka, idan akwai abubuwan da aka tsara don kyautata rayuwar jama'a, ya sami yin amfani da su. Kowane mutum na da hakkin ya kafa ƙungiyoyin kiyaye sharuɗan sana'arsa tare da makamantansan.
50 Kuma waɗanda za su shafi ƙasa ɗaya ko ƙasashe da yawa domin ko'ina a duniya jama'ar ƙasashen da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙunsa da ta ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkin waɗansu daga cikinsu ta karɓi wannan jawabi, ta kuma yi amfani da shi yadda ya kamata.
51 Wannan ya biyo bayan dakatar da sakin wasu fina-finai da Humar a yi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya. A wata sanarwa da ƙungiyar masu shirya fina-finai ta jihar Kano MOPPAN ta fitar ta ce sun yi wani zama da shugabannin hukumar inda aka cimma matsaya.
52 WTC Abuja, lokacin da aka kammala, zai zama ci gaba mafi girma a cikin yankin Yammacin Afirka. Ci gaban Cibiyar Ciniki ta Duniya Abuja ya fara ne a cikin shekara ta 2010, a kan girman ƙasa sama da hekta 6,000 a cikin Gundumar Kasuwanci ta Tsakiya ta Abuja.
53 Ganin cewa muhimmin abin da zai sa a cika wannan alkawali shi ne, dukkan ƙasashen duniya su zamanto da huska ɗaya za su hangi waɗannan hakkokin ’yan-adam da abubuwan da ’yancinsu ya ƙunsa, Majalisar Ɗinkin Duniya, a zaman taronta na gaba-ɗaya ta faɗi cewa.
54 Ya kamata ilimi ya kawo fahimtar juna da ragowa da aminci tsakanin ƙasashe da tsakanin ’yan-adam, kome launin fatarsu da addinin da suke bi, ya kuma ƙarfafa ƙoƙarin da Majalisar Ɗinkin Duniya take yi domin a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
55 Tare da layin, daga baya an fadada ikon aikin zuwa wani nau'i mai amfani da yawa, "wanda zai kasance mai cike da rana da dare". Shugaba Goodluck Jonathan ya fara aikin ne a watan Satumbar 2011, tare da kimanta kammalawa da ranar budewa da aka shirya don 2013.
56 Sauran abokan hulɗa da masu ba da shawara na aikin sun haɗa da: Kamfanin Abuja Investments wanda shine abokin tarayya, WSP Consulting shine mai ba da shawara kan tsarin, Edifice Consultants PVT Limited shine babban gine-gine, da kuma mai ba da Shawara na MEP.
57 Da farko an shirya bude shi a cikin 2013, Cibiyar Ciniki ta Duniya Abuja yanzu an shirya bude ta a cikin 2016. Cibiyoyin hada-hadar kuɗi masu zaman kansu ne ke tallafawa hadaddun, da kuma masu saka hannun jari masu zaman kansu, wanda ke da kimanin biliyan 200.
58 In kana ma mutane Magana mai dkyau zasu dinga son mu’amala da kai domin sunsan cewa zasu ji daɗi a yayin Magana da kai kuma baza su ji haushi ko baƙin ciki ba. Idan mutum ya iya Magana da mu’amala mai kyau to iya wannan ma kaɗai ya wadatar da shi a zamantakewa.
59 Ganin cewa ya kamata a kafa hukumomi waɗanda za su kula da kiyayewa da hakkokin ’yan-adam, ta hanyar girka dokoki, domin kada tsananin iko da danniya su yi yawa har su kai mutane ga yin kara ko yin tawaye, ganin cewa ya kamata a ƙarfafa aminci tsakanin ƙasashe.
60 Kuma domin ɗa'a da kyakkyawan shirin jama'a da jin daɗin rayuwa ga kowa su tabbata kamar yadda ya kamata. Ta kowane hali ba za a iya yin amfani da waɗannan hakkoki da abubuwan da ’yanci ya ƙunsa ba a cikin saba wa manufar Majalisar Ɗinkin Duniya da ka'idodinta.
61 "Tunda dai na gama NYSC ban sami aiki ba, na gwada nema a wurare, ban samu ba, yanzu ina aiki ne a wani shagon sayar da kayan sawa, yanayin aikina yana sa ni yawan magana da kwastomomi, wataƙila nan gaba zan samu babban aiki" in ji ta. Me masana ilimi ke cewa?.
62 Ba wanda za a ɗaure saboda ya aikata kuskure ko wani abu wanda dokar ƙasa ko ta ƙasashen duniya ba ta maida laifi ba a lokacin da ya aikata shi, ko da daga baya ya zama babban laifi. Haka kuma, ba za a yi wa mutum hukunci fiye da yadda dokar da ke ci a lokacin.
63 2. Kowane mutum na da hujjar cin moriyar dukkan abubuwan da ’yanci ya ƙunsa da dukkan hakkokin da aka bayyana a cikin wannan jawabi ba tare da bambanci ko kaɗan ba, ko na launin fata, ko na zama mace wala namiji, ko na harshe, ko na addini, ko na ra'ayin siyasa.
64 Aikace-aikace na igiyoyin rediyo waɗanda ba su haɗa da watsa raƙuman ruwa masu nisa ba, kamar dumama RF da ake amfani da su a cikin hanyoyin masana'antu da tanda na microwave, da amfani da likitanci kamar na'urorin diathermy da MRI, yawanci ba a kiran su rediyo.
65 11. Duk mutumin da aka tuhuma da aikata wani laifi, zai kasance da matsayin mara-laifi sai bayan an yi masa shari'a a gaban idon jama'a wadda ta nuna cewa ya taka doka, ya zamanto kuma a lokacin shari'ar an tabbatar masa da kariya wadda za ta kasance maceciyarsa.
66 Kuma za su kasance da hakkoki na namiji daidai da na mace a game da wannan aure, a cikin zaman auren ko a lokacin rabuwa idan ta faru. Ba za a ɗaura auren ba sai kowane daga cikin angwayen ya bada yardarsa cikin ’yanci. Shi dai iyali shi ne muhimmin tushen jama'a.
67 A wata sanarwar bayan taro da ƙungiyar ta fitar, ta ce lokaci ya yi da ya kamata a kawo ƙarshen rikicin na Sudan da kuma kare fararen hula yayin rikicin. Zuwa yanzu rikicin Sudan ya hallaka mutane kusan dubu 100, yayinda sama da miliyan 4 suka haƙura da muhallansu.
68 Ya ƙara da cewa akwai wasu malamai ma da basu da ilimin yin amfani da kwamfuta balantana a ce su ma ɗalibai su iya amfani da ita har ayi tunanin su ci jarabawa. "Ya kamata gwamnati ta bai wa malamai horo ta ɓangaren amfani da kwafutoci saoda ɗalibai su ma su ƙaru."
69 Ya kammala karatunsa a shekarar 2022 kuma yanzu yana koyarwa a wata makarantar Islamiyya. Kodayake yana godiya da samun aiki, har yanzu burinsa da mafarkinsa shi ne ya zama lauya. Blessing Chidera daga Abuja tana so ta zama masaniya halayyar ɗan adam 'psychologist'.
70 A tsakiyar 1890s, ginawa a kan fasahohin masana kimiyya suna amfani da su don nazarin raƙuman ruwa na lantarki, Guglielmo Marconi ya ƙera na'urar farko don sadarwar rediyo mai nisa, yana aika saƙon lambar Morse mara waya zuwa wata tushe mai nisan kilomita daga 1895.
71 10. Kowane mutum na da hakki a zaman daidai da kowa, na kotu adali kuma mai zaman kansa wanda aka kai ƙararsa a gabansa ya saurari maganar mutumin a cikin adalci kuma a gaban idon jama'a, domin kotun nan ne zai ƙayyade masa hakkokinsa da nauyin da ya rataya a wuyansa.
72 Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Shugaban Kungiyar MOPPAN ta Jihar Kano Ado Ahmad Gidan Dabino, ta ce bayan doguwar tattaunawa da shugaban Abba Al-Mustapha da wasu daga cikin ma'aikatansa da wakilai na masana'antar Kannywood, an samu matsaya a kan dakatar da fina-finan.
73 Cibiyoyin hada-hadar kudi masu zaman kansu ne ke tallafawa hadaddun, da kuma masu saka hannun jari masu zaman kansu, wanda ya kai kimanin biliyan 200. The churchgate Group, wani kamfani na gidaje na Najeriya, yana haɓaka shi, tare da Woods Bagot a matsayin mai tsarawa.
74 Sutura mai rufe tsiraici da tsafta: Zamantakewa ta wayewa na buƙatar sanya kaya masu kyau, ba lallai sai suna da tsada ba, indai suna da tsafta to ya wadatar in kuma akwai hali a iya a siya masu tsadan, amman almubazzaranci da kuɗi koda kaya ba wayewa bane illa rashinta.
75 Suka maye gurbin ta da ta jam'iyyar APC, ya ce ai dama siyasa tsari ne na bani gishiri in baka manda. Sanata Kawu Sumaila, ya ce a mazabar da yake wakiltar an masa alkawarin gyaran hanya da kawo abubuwan cigaba, kuma zance na gaskiya babu wanda hakan ba zai farantawa ba.
76 Kan gamu da cikas sakamakon rashin samun maki da ya dace da fannin da suka nema. Wannan na tilasta musu sauya fanni ko ma barin burin gaba ɗaya. "Bayan na gama bautar ƙasa, ban samu aiki ba, kuma aiki ta fannin abin da na karata wato Biochemistry yana wahala a Najeriya,".
77 Kowane taliki, da ƙoƙarin ƙasarsu da taimakon ƙasashen duniya, ya ci moriyar hakkokinsa na samun biyan buƙatunsa game da tattalin arziki, da jin dadin jama'a, da al'adu, domin waɗannan abubuwa ne ke tabbatar masa da mutunci kuma suke ɗaukaka darajar halittarsa cikin walawa.
78 "Na yi kuka da na ga sakamakon makin JAMB ɗina. Na san babu yadda zan yi na ƙaranci kwas ɗin Lauya " in ji shi. A maimakon haka ya ce aka ba shi shawara ya sauya kwas zuwa na addinin Musulunci sai idan shekara ta zagayo, sai ya sayi wani sabon fom na JAMB ya sake neman lauya.
79 Kamfanin First Intercontinental Properties Limited ne ke haɓaka shi, wani reshe na The churchgate Group, kamfanin mallakar Najeriya, kuma Woods Bagot ne ya tsara aikin, WSP Consulting shine mai ba da shawara kan tsarin, yayin da Abuja Investments Company kuma abokin tarayya ne.
80 Masanin ilimi, Dr Abubakar Yakubu ya shaida wa BBC cewa JAMB na da tasiri matuƙa a wurin sauya ɗabi'ar yaro da burin abun da yake son ya karanta ko ya zama idan ya girma matuƙar bai sami makin JAMB ɗin da kwasa-kwasan fannin abin da yake so ya karanta ba da jami'o'i suka fitar.
81 Najeriya ke yi daga jam'iyyun adawa zuwa jam'iyyar da ke kan gwamnati na cigaba da jan hankali da raɗe-raɗi tsakanin masu zargin ruwa ba ta tsami banza. Bayanai daga galibin al'umma na ƙara fitowa, inda wasu ke cewa ƴan adawa masu sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki a Najeriya.
82 Ko kuma bambancin ra'ayin da ya shafi ƙasarsu, ko na zaman jama'a, ko na arziki, ko na haifuwa, ko na wani hali daban. Bayan haka, ba za a gwada wa mutum wani bambanci ba saboda matsayin ƙasarsu ko yankinsu a fannin siyasa ko na hukunce-hukuncen shari'a ko a huskar ƙasashen duniya.
83 Har ila yau yana da hakkin a sama masa abin da zai biya waɗannan buƙatu da shi idan ya rasa aikinsa, ko yana rashin lafiya, ko wani musakanci ya same shi, ko yana cikin gwaurancin mutuwa, ko tsufa, ko wata ta'adi ko wani hatsari ya raba shi da dukiyar da ya tanada yake rayuwa da ita.
84 Kowa zai yi amfani matuƙa da hakkokinsa da abubuwan da ’yancinsa ya ƙunsa ba tare da wata iyaka ba, sai fa wadda doka ta kafa musamman domin a cikin zaman jama'a wadda ta san ma'anar dimukiraɗiyya, kowa ya san kuma ya kiyaye da hakkokin makamantansa da abubuwan da ’yancinsu ya ƙunsa.
85 "Sai na fara haɗa man shafawa da sabulu da kayan gyara jiki. Ina ganin mutane sun fara so kuma suna siya, kawai sai na ci gaba, ban taɓa shirya zama mai kula da fata ba. Mafarkina shi ne saka farin rigar likitoci, ina taimaka wa marasa lafiya ina ba su kulawa" Maryam ta ƙara da cewa.
86 Ta hanyar daidaitawa siginar rediyo (yana burge siginar bayanai akan igiyar rediyo ta hanyar bambanta wani bangare na kalaman) a cikin mai watsawa. A cikin radar, ana amfani da su don ganowa da bin diddigin abubuwa kamar jirgin sama, jiragen ruwa, jiragen sama da makamai masu linzami.
87 25. Kowane mutum na da hakkin ya sami isasshen halin da zai rayu da shi domin ya kiyaye lafiyarsa da shi da iyalinsa, da jin dadin rayuwarsu, ya kuma mallaki halin tabbatar musu da abinci da tufafi da mahalli da magani daga likita da sauran abubuwan kyautata rayuwa waɗanda suke buƙata.
88 Dr Abubakar ya kuma ce ga iyayen da ke kai hanzarta shigar da yaransu jami'o'i a halin kuma yaran ba su kai matakin rubuta JAMB ba, ya kamata su sake nazari, saboda yara na buƙatar gama sakadire kafin ya ce za iya rubuta JAMB. Ya shawarci yara da su dage da karatu domin su ci jarabawa.
89 Da ƴan ƙasar suka fi samun takardar shaidar zama ƴan Amurka, yayin da ta sanya ta a mataki na 15. Samun takardar shaidar zama ɗan ƙasa a Amurka kai tsaye tana nufin mutum ya zama ɗan ƙasar kuma zai mori kusan dukannin romon da ƴan ƙasa ke mora ƙarƙashin dokokin ƙasar, ciki har da zaɓe.
90 Kuma yana mai kyautata mu’amalarshi dasu, kuma suma suna masu kyautata mu’amalar su da shi. Wannan shi ake cema Zamantakewa ko wayewa, ko ace ma mutum ya waye. Mutum yana zama wayeyye ne ta hanyar saukin fahimtar sa da kuma yawan adadin mutane ko wuraren da ya taba mu'amalanta ko shiga.
91 A matakin ra'ayi na aikin, an yi ƙoƙari biyu da ba su yi nasara ba don tabbatar da abokan haɗin ci gaba kafin a sami First Continental Properties Limited a cikin 2009 ta hanyar tsarin tayin wanda daga ƙarshe ya haifar da yarjejeniyar haya tare da Abuja Investments Company Limited (ACIL).
92 Idan kana mu’amala karinga tattausawa, in aka tsananta maka na farko ka maida tattausan mu’amala har sai in an tsananta ne sai ka nuna tsayuwan dakan ka, domin kar a raina ka ko kuma a cuce ka. Magana mai daɗi: Zamantakewa ta wayewa na buƙatar yin Magana mai taushi da daɗin ji a gurin kowa.
93 Zamantakewa, na nufin tarayyan ɗan Adam tsakaninsa da mutane, ƴan uwansa da abokansa, daga lokacin da yake cikin ƙuruciyar sa har zuwa girmansa. Zamantakewa na farawa ne daga kuruciyan yara ko suzama mai jin magana ko kuma mara jin magana, Sannan ya shiga samartaka har izuwa dattijantakansa.
94 "Kuma akwai abubuwa da dama da na nema da aka mun, don haka me zan zauna bata lokaci. Ai ba tsarin ƙungiya ko wani gungu ba ne." Sanata Sumaila ya kuma yi zargin cewa baya ga irin su da suka fito fili suka bayyana inda suka dosa a siyasance, akwai wasu da suka ɗauki salon Angulu da kan Zabo.
95 'Na so na karanci fannin shari'a amma...' Labarin Ibrahim Musa daga Kano ma haka yake inda yake da burin zama lauya amma daga ƙarshe ya karanci fannin ilimin addinin Musulunci. Ibrahim ya rubuta jarabawar JAMB a shekarar 2018 inda ya samu maki 174, makin da bai kai a ba shi kwas ɗin lauya ba.
96 Ko kiɗe-kiɗe ko wa'azi da dai sauran su, tun lokaci mai tsawo daya wuce ana amfani da rediyo domin sauraren labarai da wasu mahimman abubuwa, rediyo na ɗaya daga cikin hanyoyin da suka fara baiwa mutane damar sanin haƙƙoƙin su a duniya dama sanin abinda ƙasashen duniya ke ciki na yau da kullum.
97 Ilimi na Zamantakewa da na addini: zamantakewa ta wayewa na bukatar ilimi mai dunbin yawa na Zamantakewa dana boko dana addini. Idan mutum ya samu ilimi to yana kaiwa makura a fannnin wayewa, ta yanda baza’a a iya taba shi ba ta kowane fuska. Nuna soyayya da boye kiyayya. Yawan tunani da nazari.
98 Cibiyar Ciniki ta Duniya wani haɗaɗɗen gine-gine ne guda takwas da ake ginawa a Gundumar Kasuwanci ta Tsakiya ta Abuja, FCT a Najeriya. Akwai gine-gine bakwai da aka tsara don shafin, biyu daga cikinsu an riga an kammala su, tare da sauran ko dai a cikin gini ko a matakai daban-daban na ci gaba.
99 Akwai ma majiyoyin da ke cewa wasu 'yansiyasar da ke kan mulki ana musu alkawarin tazarce, shiyasa suke ruguwa jam'iyyar APC domin samun sauki a zaben 2027. Amma a tattauanwarsa da BBC daraktan yaɗa labaran ofishin jam'yyar APCn na ƙasa, malam Bala Ibrahim ya ce babu gaskiya a cikin wannan zargi.
100 "Kawai na amince na karanta wannan kwas ɗin ne ba da son raina ba, na ga yawancin waɗanda muka gama karatun sakandire da su duk sun shiga jami'a, kuma ba na son na ɓata lokaci". A yanzu dai tana da shekara 28 kuma ta kammala karatun Biochemistry amma kuma tana sana'ar kayan kula da fata a Kaduna.
101 Dr Abubakar ya ƙara da cewa saboda suna ji kamar rayuwarsu a ƙare ta ɓangaren karatu." Tasirin samun ƙarancin maki a JAMB in ji Dakta ɗin ka iya sanya yaro ya ɓata lokaci sosai kafin ya gama karatu saboda wasu da su canza kwas ɗin da suke so gwanda su jira su wata shekarar su sake rubuta JAMB ɗin.
102 30. Ba wani mataki a cikin wannan jawabi, wanda wata ƙasa ko wata ƙungiya ko wani mutum zai yi amfani da shi, ya kwatanta cewa matakin ya ba shi ikon tafiyar da wata hidima, ko aikata wani abu da nufin rushe waɗannan hakkoki da abubuwan da ’yanci ya ƙunsa, waɗanda aka bayyana a cikin wannan jawabi.
103 Igiyar radiyon da na'urar watsawa ta radar ke fitarwa yana nuna abin da aka yi niyya, kuma raƙuman ruwa da ke fitowa suna bayyana wurin da abun yake. A tsarin kewaya rediyo kamar GPS da VOR, mai karɓar wayar hannu yana karɓar siginar rediyo daga tasoshin rediyon kewayawa waɗanda aka san matsayinsu.
104 Ƙididdiga ta nuna cewa a shekarar 2020 kaɗai ƴan Najeriya 8,930 ne suka sami shaidar zama ƴan Amurka, cikin 623,258 na kafatanin mutanen da suka sami wannan shaida daga sassan duniya. A Shekarar 2021, wadda ta zo da cutar Corona kuwa, mutane ƴan Najeriya 10,921 ne suka sami takardar shaidar a hukumance.
105 Ga ci-gaban kimiyya, haka kuma yana da hakkin ya yi amfani da hikimomin da da'irarsu ta tanada, da kyakkyawan sakamakon da aka samu daga kimiyya. Kowa na da hakkin a yi masa kariya ta kowane hali, domin ya sami damar yin fara'a da cin amfanin abin da ya ƙirƙiro a fannin kimiyya ko na adabi ko na hikima.
106 A cikin sadarwar rediyo, ana amfani da su wajen watsa shirye-shiryen rediyo da talabijin, wayoyin hannu, rediyon hanyoyi biyu, sadarwar mara waya, da sadarwar tauraron dan adam, a cikin sauran fa'ida, ana amfani da igiyoyin rediyo don ɗaukar bayanai ta sararin samaniya daga na'urar watsawa zuwa mai karɓa.
107 Saboda haka yana da ’yancin sake addini ko ra'ayin da ya bada gaskiya gare shi, da kuma ’yancin nuna addininsa ko ra'ayinsa, shi ɗaya ko a cikin taro kuma a fili ko a ɓoye ta hanyar koyarwa ko yin ibada, ko bauta wa abin da ya bada gaskiya gare shi da yin abubuwan da abin da yake bauta wa ɗin ya nuna masa.
108 "Ni kuma gaskiya da na koma ya saka rubuta wata JAMB ɗin gwara na haƙura da wannan, saboda sake rubuta JAMB ɗin babu tabbas." "Duk da mutane sun ce kusan kwas ɗaya ne, amma ba abin da nake son na karanta ba kenan". Blessing ta kammala karatu a 2024 kuma yanzu tana aiki a wani shagon sayar da kaya a Owerri.
109 Alaƙan mutum da sauran ƴan uwanshi ne ke nuna cikakkiyar ɗabi'ar mutum yayin da yake ma'amalantar mutane ta hanyoyin magana da aiki. Kalmar wayewa ta samo asali ne daga kalmar “Wayau” akan cewa mutane wayayyu ne kaɗai idan ya iya shiga cikin al’umma daban-daban masu banbancin halayya, ɗabi’u da kuma al’ada.

Связаться
Выделить
Выделите фрагменты страницы, относящиеся к вашему сообщению
Скрыть сведения
Скрыть всю личную информацию
Отмена